Wike: Na San Peter Obi Ba Zai Kai Labari Ba Domin Masoyansa Ba Su San Siyasa Ba

0
3

[ad_1]

  • Ministan Abuja ya bayyana cewa tun usuli ya san cewa Peter Obi ba zai iya lashe zaben shugaban ƙasa a watan Fabrairu ba
  • Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce magoya bayan Obi ba su san yanayin siyasar Najeriya ba
  • Kalaman ministan na zuwa ne kwana ɗaya tal bayan Kotun sauraron karar zaben shugaban ƙasa ta yanke hukuncinta

FCT Abuja – Ministan babban birnin tarayya (FCT Abuja), Nyesom Wike, ya yi ikirarin cewa magoya bayan Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa na Labour Party, ba su san siyasa ba.

Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma babban jigon PDP ya yi wannan ikirarin yayin hira da gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba, 2023.

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Wike: Na San Peter Obi Ba Zai Kai Labari Ba Domin Masoyansa Ba Su San Siyasa Ba
Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Kalaman Ministan na zuwa ne awanni 24 bayan Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu a zaben 2023.

Jaridar The Nation ta rahoto Wike na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Tun farko dama na san Peter Obi ba zai samu nasara a zaɓe ba, bari na faɗa muku gaskiya, ni bana ɓoye-ɓoye, a ganina zaɓen nan da ya wuce ya yi zafi, jinjina ga INEC.”

“Eh to a matsayinsa na matashi, wasu mutane zasu so a ce shi ne ya samu nasara, to amma ku duba yadda ƙuri’un da aka kaɗa suka nuna. An samu yanayin sauyi na zamani, matasa sun gaji.”

“Saboda haka a tunaninsu kawai su dangwala wa Obi kuri’unsu domin shi ne matashi idan aka kwatanta da sauran ‘yan takara. Amma abinda ba su sani ba, ba haka siyasar Najeriya take ba.”

Wike ya ƙara da cewa matasan da ke goyon bayan Peter Obi ba su san siyasa ba domin ba su san cewa kabilanci da addini na taka rawa a siyasar Najeriya ba.

A cewarsa, cancantar ɗan takara kaɗai ba zata kai shi ga nasara ba a yanayin siyasar da ake murza a wa a ƙasar nan.

Adamawa: Abinda Ya Sa Muka Sa Hoton Gwamna a Buhunan Shinkafa, Amos

Kuna da labarin Gwamnatin jihar Adamawa ta yi ƙarin haske kan dalilin sanya hoton gwamna Fintiri a jikin buhunan Shinkafar tallafi

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya tura wa jihohi kuɗi da kayan abinci domin raba wa yan Najeriya su rage radaɗin cire tallafin fetur.

Asali: Legit.ng



[ad_2]

Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here