Bana nema ta dole- Peter Obi ya sanar da matsayin takarar sa ta shugaban kasa a 2027 – Dimokuradiyya

0
2


Ba na yanke kauna ba – Peter Obi ya bayyana matsayin shugaban kasa a 2027

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi a ranar Laraba ya bayyana cewa ba shi da burin a dole sai ya zama shugaban kasa a 2027.

Obi ya ce kawai yana son fitar da talakawa da ‘yan Najeriya masu karamin karfi daga cikin mawuyacin halin da suke ciki.

KARANTA WANNAN LABARIN:APC ce kaɗai maganin matsalolin Najeriya – Ganduje

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, tsohon gwamnan jihar Anambra, ya koka kan yadda wasu ke kauracewa tattaunawa kan matsalolin da suka addabi Najeriya.

“Muna rayuwa ne a tsarin da ake ganin masu rike da mukaman gwamnati da ‘yan siyasa ne kawai a lokacin zabe ake ganin su. Zan iya gaya muku cewa aiki ne na yau da kullun. Na sha fadin cewa ba ni da burin dole sai na zama shugaban Najeriya. Amma ina sha’awar ganin an fitar da talakawa da ‘yan Najeriya marasa galihu daga halin da suke ciki a kullum.

“Abin da nake ɗokin gani ke nan. Kuma dukanmu za mu iya yin hakan ma. Ba za ku iya yin farin ciki ko gamsuwa ba yayin da miliyoyin (‘yan Najeriya) ba su san inda za su ci abinci na gaba ba,” in ji shi.

A wani labarin kuma:APC ce kaɗai maganin matsalolin Najeriya – Ganduje

Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya ce jam’iyyar za ta samar da hanyoyin magance kalubalen da ke addabar kasar nan.

Ganduje ya bayyana haka ne a yayin babban taron yakin neman zaben karshe da mika tutocin jam’iyyar APC ga ’yan takarar shugabannin kananan hukumomi 11, ranar Laraba a Gombe.



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here