Yan Najeriya Sun Fusata Yayin da Shugaba Tinubu Ya Umarci Gwamnan PDP Ya Canza Kasafin 2024

0
4


  • Tsoma bakin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a rikicin siyasar jihar Ribas ya bar baya da ƙura a kafafen sada zumunta
  • Wasu ƴan Najeriya sun nuna damuwarsu bisa yadda Gwamna Fubara ya aminta da yarjejeniyar da aka cimma a Villa da Wike
  • Tinubu ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara, Nyesom Wike, Peter Odili da wasu masu ruwa da tsaki a Villa, kuma an warware rikicin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al’amuran yau da kullum

FCT Abuja – An umarci Gwamna Siminalayi Fubara ya koma majalisar dokokin jihar Ribas ya sake gabatar da kasafin kuɗin 2024 a gaban dukkan mambobin majalisar.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wannan na ɗaya daga cikin yarjejeniyar da aka cimmawa a zaman sulhu da sauran masu ruwa da tsaki a Aso Villa ranar Litinin.

Kara karanta wannan

“Dalilin da ya sa na kulla yarjejeniya 8 da Wike”, Gwamna Fubara Ya Magantu

Sulhunta rikicin jihar Ribas.
Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Tinubu Ya Umarci Gwamnan PDP Ga Sake Gabatar da Kasafin 2024
Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bayan haka kuma gwamnan da sauran muƙarrabansa sun amince za su janye dukkan ƙararrakin da suka kai gaban kotu dangane da danbarwan siyasar Ribas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci zaman neman masalaha a fadarsa da ke Abuja, kuma kowane ɓangare ya rattaɓa hannu a kan yarjejeniya 8.

Martanin yan Najeriya kan umarnin Fubara ya sake gabatar da kasafin 2024

Sai dai umarnin da aka baiwa Gwamna Fubara ya canza gabatar da kasafin 2024 a majalisa bai yi wa da yawan Najeriya daɗi ba. Sun maida martani a soshiyal midiya.

Legit Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra’ayoyin jama’a a manhajar X, wanda aka fi sani da Twitter.

@Kaimegalos ya ce:

“Shikenan an kwace Ribas.”

@ElozonaVictor ya ce:7

“Gwamna mai ci! gaskiya wannan mutumin ya bani kunya.”

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Shugabannin jam’iyyar PDP na ƙasa sun shiga taron gaggawa a Abuja kan abu 1

@JosephOnuorah ya wallafa cewa:

“Sim Fubara ya yi babban kuskuren da zai ci shi, gaskiya ba shi da kwarewa gaba ɗaya. Shekaru huɗu kaɗai zai yi idan ya yi sa’a. Mutane irin Wike mulki kawai suka sani.”

@adedeji_ishow ya ce:

“Rattaba hannu kan yarjejeniyar da Fubara ya yi ba yana nufin aiwatarwa bane, nan gaba komai zai fito fili.”

Malami ya tsaya takarar gwamna a Edo

A wani rahoton kuma Wani malamin addinin kirista ya ayyana shiga tseren takarar gwamnan jihar Edo a zaɓe mai zuwa na shekarar 2024.

Rabaran Andrew Obinyan ya bayyana cewa al’ummar jihar da wasu ƴan Najeriya masu kishi ne suka matsa masa lamba ya fito takara.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here