Wata Sabuwa: Jam’iyyar LP Ta Bankado Wata Kulla-Kullar Kotun Koli a Shari’ar Peter Obi da Tinubu

0
2


  • Jam’iyyar adawa ta Labour Party (LP), ta soki kotun ƙoli kan taƙaddamar zaɓen shugaban ƙasan da aka yi a Najeriya
  • Jam’iyyar LP ta ce ta ga abin kunya da takaici matuka yadda kotun ƙoli bayan sauraron ƙarar da Peter Obi ya shigar, ta “ƙi yanke wani hukunci”
  • Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa kotun ƙolin ta kasa ba ta takardun abin da ta yanke a matsayin hukunci a shari’ar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al’amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja – Jam’iyyar Labour Party (LP) a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, ta bayyana cewa jam’iyyar da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, har yanzu ba su samu takardun CTC na hukuncin kotun ƙoli ba.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama kan karar da ke neman tsige gwamnan PDP a Arewa

Ku tuna cewa hukuncin da kotun ƙoli ta yanke ya tabbatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

LP ta caccaki kotun koli
Jam’iyyar LP ta caccaki kotun koli kan shari’ar Peter Obi da Tinubu
Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Obi vs Tinubu: LP ta caccaki a kotun ƙoli

LP ta yi iƙirarin cewa kotun kolin ba ta yanke hukunci kan ƙarar da Obi ya shigar kan Tinubu ba, inda ta bayyana lamarin a matsayin abin kunya da takaici.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Umar Farouk, sakataren jam’iyyar LP na ƙasa, ya ce hakan ba abu ne da za a amince da shi ba.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“Saboda taka tsan-tsan LP a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 27 ga watan Oktoba, 2023, ta buƙaci babban magatakarda na kotun ƙoli ya ba ta takardun CTC na hukuncin da aka yanke a ɗaukaka ƙarar LP.”

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Sakkwato

“Akwai tunatarwa ta wata wasika kan hakan a ranar 8 ga watan Nuwamba 2023. Sai dai, har zuwa yau, an yi watsi da wannan buƙatar.”

Jam’iyyar LP ta lura da abin kunya da takaicin yadda kotun ƙoli, bayan sauraron ƙarar da jam’iyyarmu ta shigar, ta ƙi zartar da wani hukunci, sannan ta kasa bamu takardun duk abin da ta ɗauka a matsayin hukuncin da ta yanke.”

“Wannan keta haƙƙin jam’iyyar LP da ɗan takararta ne na samun adalci a shari’a.”

Dalilin Rashin Nasarar Atiku da Obi a Kotun Koli

A wani labarin kuma, kun ji cewa Farfesa Farouq Kperogi ya bayyana dalilin da ya sanya Atiku da Peter Obi suka kasa yin nasara kan Shugaba Tinubu a kotun ƙoli.

Farfesan ya bayyana cewa ƴan takarar biyu ba su cancanci a ayyana su a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen ba, saboda ba su samu kaso 25% na yawan ƙuri’u ba a jihohi 24.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here