‘Takardun karatun Peter Obi ma akwai rufa-rufa cikin su’ – Wasu ‘yan jam’iyyar LP

0
4
‘Takardun karatun Peter Obi ma akwai rufa-rufa cikin su’ – Wasu ‘yan jam’iyyar LP


Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar LP na Ƙasa, ɓangaren shugabancin Lamidi Apapa, mai suna Abayomi Arabambi, ya yi zargin cewa akwai ɗungushe a cikin takardun makarantar ɗan takarar shugaban ƙasa na LP ɗin, wato Peter Obi.

Arabambi ya yi wannan zargi ne ranar Laraba, a lokacin da ake wata tattaunawa da shi a gidan talabijin na AIT.

Ya yi wannan zargin ne a matsayin raddi ga taron manema labarai da Peter Obi ɗin ya gabatar dangane da kwamacalar da ke cikin takardun shaidar Tinubu na Jami’ar Jihar Chicago, Amurka.

Arabambi ya yi iƙirarin cewa ya na cikin waɗanda suka tantance Obi kafin tsayawar sa takarar shugaban ƙasa a 2023.

Ya ce sunan da ke rubuce a kan satifiket ɗin kammala Jami’ar Nsukka da Obi ya yi, ya sha bamban da sunan sa na kan katin shaidar aikin bautar ƙasa, wato NYSC.

“Ina cikin waɗanda su ka tantance Peter Obi. A fam mai lamba EC9, ya rubuta cewa ya yi Jami’ar Najeriya ta Nsukka, kuma ya kammala NYSC.”‘

Arabambi ya ce akwai ha’inci a bayanan Obi, saboda sunan sa na jami’a ya sha bamban da sunan sa na jikin katin NYSC.

A ranar Laraba PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Peter Obi ya ƙalubalanci Tinubu cewa ya fito ya shaida wa duniya ainihin sunan sa, domin ya daina zubar wa Najeriya mutunci.

“Mu ɗin ma na cikin LP ba mu san haƙiƙanin cikakken sunan Peter Obi ba. Saboda a lokacin tantancewar komai a cikin sirri ya riƙa yi, shi da Abure a garin Asaba.”

“Mun ƙyale shi mun tantance shi, saboda a lokacin mu na gaggawa ne ga lokacin wa’adin shirya zaɓen fidda gwani ya zo. Shi ya sa kawai muka kauda kai.

Sai dai kuma Daraktan Kamfen na Peter Obi, Akin Osuntokun, ya ce ƙage da sharri ake yi wa Obi, dukkan takardun karatun sa sahihai ne, kuma akwai su a kafafen sadarwa a fili, ko’ina mutum ya ke zai iya gani.



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here