Shari’ar Gwamna: Kotun Daukaka Kara Ta Kori Karar APC, Ta Tabbatar da Nasarar PDP

0
8


  • Kotun Daukaka Kara mai zamanta a Legas ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Fubara na jam’iyyar PDP a jihar Rivers
  • Hakan na nufin kotun ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar APC a jihar Patrick Tonye-Cole ya shigar kan kalubalantar nasarar Fubara
  • Ko a watan Oktoba, ita jam’iyyar APC da ta dauki nauyin Cole ta janye karar da aka shigar kan nasarar Fubara, lamarin da Cole yaki yarda da shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al’amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas – Wata Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a jihar Legas a ranar Talata ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP.

Hakan na nufin kotun ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Rivers, Patrick Tonye-Cole, ya shigar kan kalubalantar nasarar Fubara.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar PDP ta garzaya kotun koli don kalubalantar shari’ar gwamnan APC, ta koka da zaluncin kotu

Gwamna Fubara/Jihar Rivers
Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Fubara na jihar Rivers. Hoto: Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Dan takarar jam’iyyar APC wanda ya halarci zaman kotun a ranar Talata ya bukaci kotun ta umurci INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cole ya daukaka kara duk da APC ta hakura?

A watan Oktoba ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Rivers ta yi watsi da karar da Cole ya shigar na kalubalantar zaben Fubara a matsayin gwamnan jihar, Channels TV ta ruwaito.

Kotun ta yi watsi da karar tana mai cewa ita jam’iyyar APC da ta dauki nauyin Cole ta janye karar da aka shigar kan nasarar Fubara.

Sai dai shi bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba, inda dan takarar na APC ya garzaya Kotun Daukaka Kara.

Vanguard ta ruwaito kotun a ranar Talata ta ce hukuncin da kotun kararrakin zabe ta yanke tun farko ta yi dai dai, wanda ya tabbatar da nasarar da Fubara a zaben jihar.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta yi hukunci a shari’ar kakakin Majalisa a Kaduna, ta umarci sake zabe

An fara shirye-shiryen tsige Gwamnan Akeredolu na jihar Ondo

A jiya Litinin Legit Hausa ta ruwaito maku yadda ake zaman dar-dar a jihar Ondo yayin da ake sa ran majalisar dokokin jihar za ta tsige gwamnan na yanzu Rotimi Akeredolu.

Wani dan majalisa da ya zanta da Daily Trust ya ce akwai yiyuwar tsige Akeredolu a zaman majalisar na gobe tare da ayyana Aiyedatiwa mukaddashin gwamna

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here