‘Peter Obi Zai Yaudari Najeriya Kamar Yadda Ya Yi Wa Ojukwu a Baya’, Jigon APC

0
2


  • Jigon jam’iyyar APC ya caccaki dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi kan takalar Shugaba Tinubu
  • Yayin da ya ke martani yayin ganawa da ‘yan jaridu, Josef Onoh ya bayyana Obi da maci amana kuma dan siyasa maras tabbas
  • Ya ce Obi ya ci amanar uban gidansa, Dim Chukwuemeka Ojukwu da kuma jam’iyyar APGA wacce ta mishi riga da wando

FCT, Abuja – Tsohon kakakin Shugaba Tinubu a yankin Kudu maso Gabashin kasar, Dakta Josef Onoh ya zargi Peter Obi da yaudarar uban gidansa Chukwuemeka Ojukwu.

Onoh ya bayyana son mulki irin na Obi shi ne dalilin yaudarar Dim Ojukwu da kuma jam’iyyar APGA, Legit ta tattaro.

Jigon APC ya soki Peter Obi kan badakalar takardun Tinubu
Jigon APC ya yi martani ga Peter Obi kan satifiket na Tinubu. Hoto: Peter Obi, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Meye jigon APC ke cewa ga Obi kan satifiket na Tinubu?

Jigon APC ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jaridu a Abuja kan maganar da Obi ya ce Tinubu ya bayyana takardunsa ga jama’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya zargi Obi da nuna kansa a matsayin mutumin kirki yayin da ya ke amfani da hakan wurin cimma burinshi na siyasa, cewar The Nation.

Yayin da ya ke yamutsa Peter Obi, Onoh ya ce har yanzu cin amanar Ojukwu da Obi ya yi na binshi wanda ya jawo rikicin jam’iyyar Labour tsagin Lamidi Apapa.

Meye Obi ke zargin Tinubu dangane da satifiket?

Ya kara da cewa abin da ya sa Obi ke ta fada yanzu shi ne duk jam’iyyunsa na baya sun juya masa baya da su ka hada da APGA da PDP da kuma LP.

Peter Obi na kalubalantar zaben Tinubu da kuma takardun bogi da ake zargin ya mika wa hukumar zabe ta kasa, INEC.

A cikin wata ganawa da ‘yan jaridu, Obi ya bukaci Tinubu da ya sake gabatar da kansa ga ‘yan kasar.

Jigon jam’iyyar LP ya fadin dalilin dukan da Obasanjo ya mishi

A wani labarin, kakakin jam’iyyar Labour, Abayomi Arabambi ya bayyana dalilin da ya sa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya mishi dukan tsiya.

Abayomi ya ce ya tsaya tsayin daka don ganin ya fallasa wata badakala amma Obi da Obasanjo su ka ce ya bari sai Peter Obi ya ci zabe tukun a shawo kan matsalar.

Ya ce dalilin kin amincewa da bukatar tasu ce ta sa Obasanjo ya dake shi a cikin gidansa.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here