Obi Vs Tinubu: Malamin Coci Kingsley Okwuwe Ya Ce Peter Obi Zai Amshe Kujerar Tinubu

0
3


  • Dan takarar jam’iyar Labour a zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata ya shigar da ƙara kan zaɓen
  • Fasto Kingsley Okwuwe na cocin ‘Revival and Restoration Global Mission’ ya bayyana wahayin da aka yi masa
  • Malamin ya hasaso cewa kotu za ta sauke Tinubu, kuma Peter Obi ne zai maye gurbinsa

FCT, AbujaFasto Kingsley Okwuwe na cocin ‘Revival and Restoration Global Mission’, ya bayyana cewa ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar Labour wato Peter Obi, zai cika burinsa.

Fasto Okwuwe ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya ɗora a shafinsa na YouTube.

Malamin coci ya faɗi yadda Peter Obi zai karbe kujerar Tinubu
Fasto Kingsley Okwuwe ya ce Peter Obi zai dare kujerar Tinubu. Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Peter Obi zai zama shugaban ƙasa

Faston ya bayyana cewa ya gani a wahayin da aka yi ma sa cewa Peter Obi zai zama sabon shugaban ƙasa, a yayin da Najeriya za ta dawo sabuwa.

Kara karanta wannan

An Kuma Yin Juyin Mulki a Wata Kasar Afrika Ta Yamma Ta Daban? Bayanai Sun Fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce Bola Tinubu zai tafi a yayin da Peter Obi zai zo domin ya ɗare kan kujerarsa.

Ya ƙara da cewa kujerar da Tinubu yake kai a yanzu ba halastacciya ba ce, kuma Peter Obi zai yi nasara kansa a kotu.

Peter Obi dai ya shigar da ƙarar Shugaba Tinubu ne a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, inda yake ƙalubalantar nasarar da ya samu a zaɓen da ya gabata.

Shehu Sani ya ƙalubalanci Atiku kan ci gaba da shari’a Tinubu

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan martanin da tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu ya yi kan karɓar muƙamin da tsohon gwamnan Ribas Nyesom Wike ya yi.

Shehu Sani ya ce bai kamata Atiku Abubakar ya ci gaba da shari’a da Shugaba Bola Tinubu ba tunda ɗan jam’iyyarsu ya karɓi muƙami a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Kaico: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Malamin Addini Har Lahira a Jihar Kaduna

Nyesom Wike dai na daga cikin ministoci 45 da da shugaba Bola Tinubu ya naɗa a matsayin waɗanda za su taya shi tafiyar da gwamnatinsa.

Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin sako ga ministocinsa

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da shugaba Bola Tinubu ya aike ga sabbin ministocinsa da ya naɗa.

Shugaba Tinubu ya ce shi da ministocinsa kamar matafiya ne a cikin jirgi ko mota, amma dai shi ne direban.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here