Nasarar Tinubu a Kotun Koli: APC ta Aikawa Atiku, Peter Obi Sakon Gaggawa

0
3


  • An bukaci manyan abokan hamayyar Shugaba Bola Tinubu su hada hannu da shi domin ceto Najeriya
  • An shawarci Atiku Abubakar da Peter Obi su goyi bayan gwamnatin tarayyar Tinubu kuma su bada shawarwari kan cigaban Najeriya
  • Jigon APC, Francis Okoye, ne ya bada wannan shawarar yayin martani kan hukuncin kotun koli wacce ta jadada nasarar Tinubu, ta yi watsi da karar Atiku da Obi kan rashin inganci

FCT, Abuja – Biyo bayan hukuncin kotun koli, an bukaci Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da takwararsa na jam’iyyar Labour, Peter Obi su mayar da takkubansu su yi sansanta da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Jigon APC ya bai wa Atiku, Peter Obi muhimmin shawara
Jigon APC, Francis Okoye, ya shawarci Atiku da Peter Obi su mara wa Tinubu baya. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Jigon APC ya aika sako ga Atiku, Peter Obi bayan nasarar Tinubu a Kotun Koli

Idan za a tunawa, kotun mafi girma a kasa, a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, ta yi watsi da daukaka kara da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku da Obi suka shigar na kallubalantar zaben Tinubu da aka yi a watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun koli: A karshe Tinubu ya maida martani ga kalaman Atiku Abubakar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hukuncin kotun, ta jadada nasarar Tinubu, ta kawo karshen dukkan cece-kuce da suka taso kafin, yayin da bayan zaben shugaban kasa na 2023.

A wani hira ta musamman da Legit.ng, a ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba, shugaban kungiyar yan APC na Kudu maso Gabas, Francis Okoye, ya jadada cewa zabe ya wuce, kuma yanzu lokaci ne na fara aikin gwamnati.

Ya yi kira ga sauran yan takarar shugaban kasa da su hada hannu su tallafawa gwamnati mai ci a yanzu yayin da ya ke cewa shawararsu za su yi amfani da Shugaba Tinubu.

Okoye ya bayyana wasu muhimman matakai da Atiku da Obi za su iya dauka don inganta siyasarsu bayan hukuncin Kotun Koli wacce Tinubu ya yi nasara.

Jigon na APC ya ce:

“Zabe ya zo kuma ya wuce, lokaci ne na aikin gwamnati da tsarin ‘Renewed Hope’ da 8 point agenda ta gwamnatin Tinubu don haka yana bukatar dukkan goyon baya daga manyan masu ruwa da tsaki, abokan hamayya da yan kasa.

Kara karanta wannan

Babu inda zan tafi, Atiku ya magantu kan mataki na gaba bayan hukuncin kotun koli

“Zan shawarci babban yayana Peter Obi na jam’iyyar Labour da Atiku Abubakar na Peoples Democratic Party su mayar da takkubansu kuma su goyi bayan gwamnati mai ci yanzu domin yi wa yan Najeriya aiki.

“Su bada shawarwari masu amfani ga Shugaban Kasa domin ya yi nasara. Idan har suna nufin Najeriya da alheri kamar yadda suke ikirari lokacin kamfe, su nuna hakan ta hanyar bai wa shugaban kasa shawarwarin da za su inganta kasa.

“Kadu su boye basirarsu. Kada Atiku ya koma Dubai da shawarwarinsa ya jira sai 2027 ya sake takara. Muna bukatar shi yanzu. Daga karshe, hamayya na da kyau don ganin gwamnati ta tsaya tsayin daka. Don haka su kasance abokan hammaya masu amfani ga gwamnatin APC amma ba abokan hammaya na wofi ba.”

Kotu ta yi fatali da bukatar Atiku Abubakar

Tun a baya an rahoto cewa kotun koli a ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba, ta yi fatali da bukatar Atiku Abubakar na gabatar da sabbin shaidu kan kararsa na kallubalantan nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Shiga Yar Buya Bayan Ya Sha Kaye a Kotun Koli? Kakakin Kamfen Din LP Tanko Ya Magantu

A cewar Channels TV, Kotun Koli ta fadawa Atiku, dan takarar shugaban kasa na PDP cewa kwanaki 180 da aka ba su damar gabatar da sabbin shaidu sun wuce.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here