Najeriya Kuma Ba a Koshi Ba: Kasar Kenya Ta Kera Wayoyin Hannu, Ana Ba ’Yan Kasa Bashi

0
3
Najeriya Kuma Ba a Koshi Ba: Kasar Kenya Ta Kera Wayoyin Hannu, Ana Ba ’Yan Kasa Bashi


  • Shugaban kasar Kenya ya rantsar da wasu wayoyin hannu na zamani da aka kera a kasar a farashi mai rahusa
  • Shugaba William Ruta ne ya jagoranci wannan rantsarwa a kamfanin da ya kera wayoyin a yankin Mayako, Machakos a kasar
  • A watan Mayun 2023 ne kamfanin Safaricom ya alanta fara aikin kera waya a kasar, inda ake hasashen kera wayoyi miliyan 1.4 a shekara

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al’amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Kenya – An buga wayoyin hannu na zamani a kasar Kenya, an saka musu suna Neon Smarta da kuma Neon Ultrav da ake siyarwa a farashin $50 (N38,807).

An kera wayoyin ne a hadin gwiwa tsakanin kamfanin Safaricom da Faiba da kuma gamayyar hada na’urori a Gabashin Afrika, EADAK.

Kara karanta wannan

Shugabannin NNPP a Arewa maso Yamma sun yi zama kan batun korar Kwankwaso a jam’iyya

An kera waya a kasar Kenya
An kaddamar da wayar da aka kera a Kenya | Hoto: SafaricomPLC
Asali: Facebook

EADAK, karkashin jagorancin shugaba William Ruta ne ta rantsar da wayoyin a ranar 30 ga watan Oktoba, inda aka ce za a iya samar da wayoyi 21,000 duk wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya wayar Kenya take?

Bayanan fasaha sun bayyana cewa, Smarta ce karamar waya mai girman inci 5 idan aka kwatanta da Ultra da ke da girman inci 6.5 a allo.

An kuma ruwaito, dukkan nau’ikan wayoyin biyu suna da RAM 2GB da kuma ma’ajiyar bayanai da girmansa ya kai 32GB. Hakan nan, suna aiki da sabis din 4G ne.

Shugaba Ruto ya tabbatarwa ‘yan Kenya cewa, gwamnatinsa za ta ba da gudunmawar da ake bukata wajen tabbatar da kera wayoyin da dama.

A cewarsa:

“Za a kera wayoyi sama da miliyan uku kuma za su kasance da araha akalla 30% kasa da kayan da ake shigo dasu.

Kara karanta wannan

Tsohuwar jarida dake nuna farashin naira kan dala a 1978 ta bayyana a intanet, jama’a sun girgiza

“Mun amince da masu ruwa da tsaki cewa wadannan wayoyi za a siyar dasu a farashin KSh 7,500.”

Yadda gwamnatin Kenya ta sa baki

Majiyoyi daga kasar sun shaida cewa, Safaricom da sauran masu ruwa da tsaki sun ba ‘yan Kenya damar ajiye KSh 1,000 domin su karbi wayar, sannan su fara biya a hankali daga watan Janairun badi.

A cewar rahoto, duk wanda ya karbi wayar, zai ke ba da KSh 20 ne a rana, wanda bai wuce N104.88 a rana.

A cewar shugabannin kamfanin Safaricom:

“Tare da hadin gwiwar Google, mun samar da wayoyi masu rahusa da za a siya a biya a hankali da muke kira Lipa Mdogo Mdogo.”

An ce miliyoyin mutane sun nuna sha’awarsu kan wannan wayoyi kuma sun fara amfani da ita tun tuni. Ina muka kwana a Najeriya?

Dan Najeriya ya kera waya

A wani labarin, John Msughter na daya daga cikin dimbin matasan Najeriya da ke baje kolin irin hazakarsu da ke da yawa a kasar.

Kara karanta wannan

“Ni ba waliyyi bane, Najeriya ba ta da matsala”, In ji Peter Obi

Mutumin mai shekaru 44, duk da cewa yana da nakasa, ya kera tare da habaka wata wayar salula da ya kira Chelsea Mobile Mate 40 Pro kuma abin daukar hankali, bai yi karau a jami’a ba.

Da yake nuna wayoyin John a Facebook, wani dan jarida da ya bayyana a matsayin abokinsa mai suna Ukah Kurugh ya bayyana cewa John dan asalin jihar Benue yana neman hadin gwiwa domin samar da wayoyin da yawa.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here