Kungiyar Lauyoyi Ta Tabbatar Da Fara Gurfanar Da Masu Laifukan Zaben 2023

0
12


Gwamnatin tarayya karkashin kungiyar lauyoyi ta Nijeriya (NBA) ta fara gurfanar da wasu jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da mambobin jam’iyyar siyasa bisa samun su da laifuka daban-daban a lokacin gudanar da zaben 2023.   

Laifukan zabe sun kasance babban barazana ga gudanar da sahihin zabe a Nijeriya, domin sukan janyo tsananin gabar siyasa da kuma haddasa rikice-rikice.

Bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun 2023, rundunar ‘yansandar Nijeriya ta ce ta samu nasarar damke mutane sama da 700, bisa karya dokokin zabe.

A ranar 2 ga Mayun 2023, INEC ta ce ta gurfanar da mutum 215 cikin mutum 774 da ‘yansanda suka kama bisa aikata laifuka daban-daban da suka shafi zabe.

Hukumar INEC ta ce ta hada kai da kungiyar lauyoyin Nijeriya domin gurfanar da wadanda aka kama bisa karya dokokin zabe a gaban kuliya.

Daga cikin shari’o’i 215 da hukumar INEC ta samu, shari’o’i’ 196 sun kasance laifuka ne na karya dokokin zabe, wanda kuma INEC da lauyoyi suke kulawa da su.

Sakataren yada labarai na NBA, Habeeb Lawal, an gurfanar da wadanda ake zargi mutum 196 ciki har da jami’an INEC da mambobin jam’iyyun siyasa, bisa karya dokokin zabe da suka hada da sayan kuri’u, mallakar makamai da sauran laifuka da suka aikata lokacin zaben 2023.

Lawal ya kara da cewa an gurfanar da wadanda ake zargin ne a kotunan majestiri da sauran manyan kotuna da ke jihohi da kuma Abuja.

Ya ce, “An gurfanar da mutum 196 da ake zargi da karya dokokin zabe, kuma mambobin kungiyar lauyoyi ne ke kula da lamarin.

“Laifukan sun hada da sakaci wurin gudanar da aiki, kada kai wajen aikata ta’addanci, kawo hagitsi a wurin zabe, fito da makami lokacin zabe, satar akwatin zabe, lalata kayayyakin zabe, yin magudin zabe, mallakar kayayyakin zabe ba bisa ka’ida ba, rashin mayar da hankali lokacin zabe, sayar kuri’a da kuma kawo rikice-rikice a lokacin zabe.

“Wasu daga cikin wadanda ake zargin jami’an INEC ne, yayin da wasu mambobin jam’iyyun siyasa ne, sannan kuma wasu kuma ba su da alaka da harkokin siyasa.

“Kotunan majestiri da ke jihohi da Abuja suke kulawa da shari’o’in da suka danganci laifukan zabe kamar yadda dokar zabe ta tanada.

“Domin haka, mambobin kungiyarmu suna kulawa da wadannan shari’o’i a dukkan fadin kasar nan,” in ji shi.



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here