Ku Shiryawa Hukuncin Kotu ranar 16 ga watan Satumba – Inji Charly Boy – Dimokuradiyya

0
11


Obi, Tinubu, Atiku: Ku Shiryawa Hukuncin Kotu ranar 16 ga watan Satumba – Inji Charly Boy

Shahararren dan wasan kwaikwayo na Najeriya, Charles Oputa, wanda aka fi sani da suna Charly Boy ya yi ikirarin cewa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta sanya ranar 16 ga watan Satumba domin yanke hukunci kan karar da ke kalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu.

Yayin da DAILY POST ba za ta iya tabbatar da ranar ba, Kotun, bisa ga Kundin Tsarin Mulki, tana da har zuwa 16 ga Satumba, 2023 (wanda shine Matsakaicin kwanaki 180 na shigar da kara) don yanke hukunci kan karar.

KARANTA WANNAN LABARIN:Jigo A Jam’iyyar NNPP Ya Fice Daga Jam’iyyar, Ya Ce Akwai Rikici A Ciki

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu da takwaransa na jam’iyyar Labour, LP, Peter Obi sun shigar da kara suna neman kotun ta kori Tinubu kan wasu zarge-zarge.

Charly Boy a cikin wani rubutu a daya wallafa a shafin sa na X, ya bukaci magoya bayan Obi da aka fi sani da Obidients su shirya don yanke hukunci.

” Kotun daukaka kara (PEPT) ta sanar da cewa an shirya ranar yanke hukunci kan kararrakin da suka hada da Peter Obi da jam’iyyar Labour a kan Bola Tinubu, INEC, Shettima, da APC, da kuma karar da PDP ta shigar da Atiku a kan APC, INEC, da Tinubu. Satumba 16, 2023.”

A wani labarin kuma:Ambaliyar Ruwa Ta Yi Awon Gaba Da Yara 2

An bayar da rahoton mutuwar yara biyu a jihar Anambra sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta afku a garin Nkwele Awka da ke karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra.

Yaran ‘yan tsakanin shekaru hudu zuwa bakwai sun rasa rayukansu a wurare biyu daban-daban a yankin.



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here