Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama a Shari’ar Neman Tsige Gwamna Mai Ci, Ta Ba da Dalilai

0
3


  • Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Alex Otti na jam’iyyar LP a matsayin gwamna
  • Kotun ta kuma yi fatali da korafe-korafen ‘yan takarar jam’iyyun PDP da APC da zargin kawo wasan barkwanci a cikin dimukradiyya
  • Ta ce kasancewar Otti dan jam’iyya ne ko akasin haka hurumin jami’yya ce kafin zabe wanda babu ruwanta a ciki

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – Kotun Daukaka Kara ta raba gardama a hukuncin shari’ar zaben Gwamna Alex Otti na jihar Abia.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Alex Otti na jam’iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zabe, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama kan shari’ar zaben dan Majalisar PDP, ta bayyana mai nasara

Har ila yau, ta yi watsi da korafe-korafen ‘yan takarar jam’iyyun PDP da APC saboda rashin isassun hujjoji.

Kotun da ke zamanta a jihar Legas ta yanke hukuncin ne a yau Asabar 2 ga watan Disamba inda ta ce ‘yan takarar APC da PDP barkwanci su ke son shigar wa dimukradiyya.

Ta kuma ce matsalar kasancewa dan jam’iyya ko sabanin haka wannan matsala ce ta jami’yya kafin zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta tattaro cewa kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Otti ne saboda zaben ya yi dai-dai da tsarin dokar hukuncin zabe.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here