Kotu Za Ta Yanke Hukunci A Ranar Laraba

0
2


  •  Za A Yada Hukuncin Kai Tsaye A Gidajen Talebijin

Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na zaben 2023 da ya gudana, za ta yanke hukuncinta a ranar Laraba 6 ga watan Satumba kan korafe-korafen da aka shigar da ke kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu. 

 

Hukuncin da za ta yanke kan karar da jam’iyyar LP da dan takararta Peter Obi da PDP da dan takararta Atiku Abubakar da  APM da suka shigar suna kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu (APC) a matsayin shugaban Nijeriya.

A wata sanarwar da rijistan kotun daukaka kara Umar M. Bangari Esq ya fitar a ranar Litinin, ya ce wadanda aka tantance ne kawai za su samu shiga cikin kwaryar kotun.

 

Ya kuma ce domin tabbatar da gaskiya da yin komai a bayyane, za a yada zaman hukuncin kai tsaye a gidajen talebijin na kasa domin al’umma su bibiya kai tsaye.

 

Sanarwar ta ce, “Kotun daukaka kara tana sanar da al’umma cewa za a yanke hukunci kan kararrakin da aka gabatar a gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa a ranar Laraba 6 ga watan Satumba, 2023.

 

Hukunci tsakanin “• CAREPC/03/2023 tsakanin Mr. Peter Gregory Obi & Anor tsakani da hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa da wasu 3.

 

“• CA/PEPC/04/2023 Allied Peoples Movement tsakaninta da hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa da wasu 4.

 

“• CA/PEPC/05/2023 Abubakar Atiku & Anor tsakani da hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa da wasu 2.”

 

“Wadanda aka tantance ne kawai ke da ikon shiga harabar kotun.

 

“Kuma daidaiku ne, ciki har da lauyoyi da wakilan jam’iyyu za su samu shiga cikin kwayar kotun.”

 

LEADERSHIP Hausa dai ta labarto cewa Tinubu ya samu kuri’u 8,794,726 kamar yadda INEC ga sanar da wadda hakan ya ba shi damar kayar da Atiku Abubakar na PDP mai kuri’u 6,984,520, da Peter Obi na Labour Party (LP) da ya samu kuri’u 6,101,533.

 

Jam’iyyu biyar ne suka nuna kin amincewarsu da sakamakon zaben sun hada da PDP, LP, Action Peoples Party (APP), Allied Peoples Movement (APM) ada kuma Action Alliance (AA) inda suka shigar da korafinsu a gaban kotu.

 

Jim kadan bayan fara sauraron kararrakin a watan Mayu, APP da AA sun janye korafe-korafen da suka shigar.

 

Daga cikin manya-manyan dalilan da masu korafin suka gabatar sun hada da cewa Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima ba su cancanci fitowa takarar shugaban kasa ba.

 

Sun yi ikirarin cewa Tinubu ya kasance mai laifin safaran kwayoyi a Amurka, shaidar karatunsa da ya gabatar wa INEC na bogi ne da kuma cewa Tinubu ya na da dan kasar Guinea ne.

 

Masu korafin sun cewa tun da Tinubu ya kasa samun kaso 25 cikin 100 a babban birnin tarayya FCT to bai kamata a ayyana sa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu ba.

 

A ranar 1 ga watan Agustan ne kotun sauraron kararrakin zaben mai alkalai 5 ta saurari jawabin karshe na lauyoyin Atiku da Obi.



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here