Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Kwankwaso Ya Aika Gagarumin Sako Ga Abba Gida-Gida

0
2


  • An bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da ya ci gaba da harkokinsa sannan ya karbi hukuncin kotun daukaka kara
  • Kotun daukaka kara ta tsige gwamnan mai ci a ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba, inda ta soke nasarar zabensa na ranar 18 ga watan Maris
  • An bukaci Abba Gida-Gida da ya hakura da zuwa kotun koli domin hujjar da ake da shi a kansa ba wanda za a iya watsi da su bane

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano – Babban jigon jam’iyyar APC, Alhaji Iliyasu Kwankwaso, ya bukaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya karbi hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige shi daga kujerarsa, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida ya magantu bayan Kotun Daukaka Kara ta tsige shi daga kujerar gwamnan Kano

Kotun ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamna na ranar 18 ga watan Nuwamba a jihar Kano.

An shawarci Abba ya yarda da shan kaye
Hukuncin Kotun Daukaka Kara: Kwankwaso Ya Aika Gagarumin Sako Ga Abba Gida-Gida Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Kwankwaso, tsohon kwamishinan raya karkara da cigaban al’umma a jihar, ya gargadi Abba Gida Gida a kan ci gaba da bibiyar shari’ar har zuwa kotun koli, musamman bayan shan kaye a kotun zabe da kotun daukaka kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta nakalto yana cewa:

“Zai zama wani babban aiki ja a gare shi ya kai shari’ar kotun Allah ya isa, duba ga hujjojin da aka gabatar kansa a kotun zabe da kotun daukaka kara, akwai bukatar ya je ya huta har zuwa 2027.”

Da yake martani ga hukuncin kotun daukaka karar kan takaddamar zaben gwamnan jihar Kanon, Kwankwaso ya yaba ma nasarar dan takarar gwamnan APC, Nasiru Yusuf Gawuna, yana mai nuni da shi a matsayin nasara ga damokradiyya da tsarin doka.

Kara karanta wannan

Bayan tsige gwamnan Kano, Malamin addini ya yi hasashen sakamakon hukuncin zaben Kaduna da Nasarawa

Kwankwaso bai ji dadin abun da Abba Gida-Gida ya yi ba

Kwankwaso ya nuna rashin jin dadinsa cewa Abba Yusuf bai amshi hukuncin kotun zaben gwamna ba kuma maimakon haka sai ya zabi karar da albarkatun kasar wajen bibiyar shari’ar a kotun daukaka kara.

Da soke zabensa da kotun daukaka kara ta yi, Kwankwaso ya bayar da shawarar cewa ya kamata Gwamna Yusuf ya mayar da hankali kan shirin sake takara a 2027 karkashin jam’iyyar siyasa mai tasiri.

Ya ce:

“A matsayina na dan uwa, ina amfani da wannan damar don shawartarsa da ya kau da duk wani yunkuri na jan batun zuwa kotun Allah ya isa amma dai ya kwana da sanin cewa lokaci bai yi ba da zai zama gwamnan jihar.”

Kano: NNPP za ta Kotun Koli

A halin da ake ciki, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta bayyana bakin cikinta game da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, da ta kori gwamnan Kano, Abba Yusuf.

Jam’iyyar ta ce za ta binciki duk wata hanya ta doka da za ta kwato mata hakkinta.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here