Gwamna Ya Dawo Zai Dauko Musulmai Bayan Nada Kiristoci Zalla a Kwamitin Tsaro a Arewa

0
6


  • Gwamnatin jihar Filato ta nada wani kwamiti da zai duba lamarin rashin tsaro da ake fama da shi
  • A kwamitin mai mutum 10, babu musulmi wanda hakan ya jawo zargin rashin adalci da gaskiya
  • Daga baya Caleb Mutfwang ya yarda zai dauko musulmai domin ganin ya tafi da kowane bangare

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Plateau – Gwamnatin jihar Filato tayi alkawari za ta tafi da kowa wajen kawo karshen matsalar tsaro da ya dabaibaye garuruwa.

Mai girma gwamna Caleb Mutfwang ya kafa wani kwamiti da zai duba lamarin tsaro a Filato, dukkanin ‘yan kwamitin nan kiristoci ne.

Gwamnan jihar Filato
Gwamnan jihar Filato Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Gwamna ya nada kwamitin kiristocin zalla

Legit ta samu takardar kafa kwamitin da ta fito daga ofishin Sakataren gwamnatin jihar Filato, Arc. Samuel N. Jatau a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Fetur zai iya kara tsada maimakon a samu sauki da matatun gida za su fara aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kwamitin na mutum 10, babu musulmi ko guda a Filato mai adadin musulmai a jihar.

Filato: Su wanene ‘yan kwamitin?

Tsohon sojan sama, AVM Napolon Bali mai ritaya wanda ya rasa kujerarsa a majalisar dattawa ne zai jagoranci kwamitin tsaron.

Kamar yadda N. Jatau ya sanar a madadin gwamna, sauran ‘yan kwamitin su ne Mai martaba Da Gyang Buba, Farfesa Gyanyir Lombin.

Sai Janar G.G. Shipi mai ritaya, DIG Felix Vwamhi mai ritaya, DIG Habila Jwalshak mai ritaya da Manjo Toholman Daffi mai ritaya.

A kwamitin akwai shugaban dakarun Operation Rainbow da wakili daga kungiyar PIDAN.

Za a sa musulmai a kwamitin

Daily Trust wanda ta fitar da rahoton ta ce shi Arc Samuel Jatau ne zai zama sakatare. Daga baya sanarwa ta nuna za a jawo musulmai.

Musulmai sun yi Allah wadai da yadda aka maida su saniyar ware a jiharsu ganin cewa wannan rikici ya shafi dukkanin manyan addinai.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Majalisar dokoki ta tabbatar da sabbin kwamishinoni 18 da gwamnan Arewa ya naɗa

Rahoton ya ce daga baya N. Jatau ya yi alkawarin za a sa musulmai cikin ‘yan kwamitin bayan jin tulin korafi daga kafafen sada zumunta.

Jawabin ya kara da cewa gwamnatin Mutfwang za ta rika damawa da kowa, tare da kira ga miyagu su guji maganganun da za su raba kai.

Matsalar rashin tsaro a Najeriya

Ana da labari jami’an tsaro da rundunar Amotekun sun shiga neman mutanen da aka sace daga makaranta a wani hari da aka kai a Ekiti.

An yi nasarar cafke wasu mutane zuwa yanzu. Duk abin da yake faruwa, Shugaba Bola Tinubu yana kasar waje, sai nan gaba zai dawo.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here