Gabon ta sanya dokar hana fita da toshe kafar sada zumunta

0
3


An kakaba dokar hana fita tare da toshe kafofin internet a kasar Gabon saboda kiyaye barkewar rikici da barin hakan zai iya haifar wa, musamman akan sakamakon zabe da ya gudana a kasar.

Wallafawa ranar:

Gwamnatin kasar Gabon ta kakaba dokar hana fita tare da toshe kafofin sadarwa na Internet a kasar a yayin da a wanin bangare kuma aka rufe rumfunan zaben shugaban kasa wanda ya gudanar a ranar asabar da ta gabatar.

Dokar hana fitar dai zata fara aiki ne daga ranar lahadin nan 27 ga wata Agustan da muke ciki daga karfe 7 na yammacin kasar zuwa 6 na Safiya kamar yadda ministan sadarwar kasar Rodrigue Mboumba Bissawou ya baiyana a kafar talabijin din kasar.

Ministan ya kuma kara da cewa an sanya dokar ce domin hana yaduwar rikice-rikice da ka iya barkewa a sanadiyar sakamakon zaben.



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here