Fasto Elijah Ayodele Ya Gargadi Atiku, Peter Obi Kan Zuwa Kotun Koli

0
6


  • Fasto Elijah Babatunde Ayodele, ya buƙaci Atiku Abubakar da Peter Obi ka da su ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun zaɓen shugaban ƙasa
  • Atiku da Peter Obi sun yi watsi da hukuncin kotun inda suka umarci lauyoyinsu da su ɗaukaka ƙara a kotun ƙoli
  • Ayodele, ya bayyana cewa wannan ɗaukaka ƙarar asarar dukiya ce kawai saboda ba ta yi daidai da abin da ubangiji ya so ya faru ba

Ikeja, jihar Legas – Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijah Ayodele, ya bayyana cewa matakin Peter Obi da Atiku na zuwa kotun ƙoli asarar dukiya ce kawai.

Primate Ayodele ya buƙaci ƴan takarar na jam’iyyun adawa da su yi amfani da kuɗin su taimaki mabuƙata a Najeriya.

Fasto Ayodele ya gargadi Atiku da Peter Obi
Fasto Ayodele ya ce yan takarar barnar kudinsu kawai za su yi a kotun koli
Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya buƙace su da fara shirin zaɓe mai zuwa a ƙoƙarin da su ke na ganin sun ƙwace mulki a hannun jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin Da Zai Faru Ga Atiku, Peter Obi a Kotun Koli

Ka da ku ɓarnatar da kuɗin ku”: Ayodele ga Atiku, Obi

Malamin addinin ya isar da saƙon ne a shafinsa na X (wanda a baya aka sani da Twitter) a ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban cocin na INRI ya bayyana cewa:

“Obi da Atiku sun gama ruɗe wa. Fastoci miliyan 10 ba za su iya cire Tinubu ba. Za ku yi mamaki, ni ba na adawa da kowanne daga cikinsu. Duk ina son su. Amma damuwa ta, ita ce akwai wasu abubuwan da ba a wasa da su.”

“A lokacin da ubangiji ya ce ‘wannan shi ne abin da na ke so’, babu wanda ya isa ya ja da kalmar ubangiji.”

“Don haka tafiyar Obi da Atiku zuwa kotun ƙoli asarar kuɗi ce, asarar lokaci ne. Ba na ganin za su samu wani abu daga kotun. Ku yi amfani da kuɗin ku taimaki jama’a, ku yi amfani da kuɗin ku ba jama’a, ta yadda ba za ku yi asarar kuɗin ku ba.”

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1 Da Yakamata Atiku/Peter Obi Su Amince Da Hukuncin Kotu

Dan Takarar LP Ya Yi Nasara a Kotu

A wani labarin na daban kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar Plateau ta soke nasarar da Peter Gyengdeng na jam’iyyar PDP ya samu a zaɓen ɗan majalisar Barkin/Riyom.

Kotun ta tabbatar da ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, Rom Chollom a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 25, ga watan Fabrairun 2023.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here