‘Dattawan Arewa ba da yawun Arewa suke magana ba’ – Matawalle

0
3


Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ragargaji Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), dangane da wata barazana da suka yi wa Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ko kuma gwamnatin sa.

Cikin wata sanarwar da Matawalle ya fitar a ranar Asabar, tsohon gwamnan Jihar Zamfara ɗin ya ce dattawan Arewa ba da yawun ‘yan Arewa suke magana ba.

Matawalle ya ce ƙungiyar NEF gungun wasu dattawa ne kawai da suke ƙware wajen gutsiri-tsoma da tsugudidin surutan da ke zubar wa Arewa da mutunci da martabar yankin.

Ya ce idan ka ji NEF na wani ɓaɓatu, to buƙatar kan su ce ko wata manufar su suke don cimmawa.

Ya ce muguwar halayyar ƙungiyar dattawan da ke kiran kan su Dattawan Arewa ta fama gundumar kowa, ya ce ba su iya bijiro da wani kyakkyawan tunanin da zai iya kawo ci gaban Najeriya a nan gaba ko a yanzu, ko su kawo wani tunanin da zai ƙara kawo haɗin kai tsakanin mabambantan al’ummomin cikin Najeriya.

Ya ce ƙungiyar na yin harbin-iska ne kawai da soki-burutsu, saboda ɗan takarar su na zaɓen 2023 bai yi nasara ba.



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here