Crystal Palace na son tsawaita zaman Eze, Man Utd za ta sayar da Sancho

0
2


xavi

Asalin hoton, Getty Images

Crystal Palace za ta buɗe sabuwar tattaunawa kan kwantiragi da take son bai wa ɗan wasanta ɗan ƙasar Ingila Eberechi Eze, wanda yanzu haka yake kan yarjejeniyar da wa’adinta ke cika a 2025.(Athletic)

Manchester United ta shirya sayar da ɗan wasanta na Ingila Jadon Sancho, da ta siya kan fam miliyan 73 da ke Borussia Dortmund, a watan Janairu. (Star)

Tottenham na nazari kan ɗan wasanta na Koriya ta Kudu mai shekara 31 da ke buga gaba Son Heung-min, wanda kwantiraginsa zai ƙare a 2026. (Telegraph)

Bayern Munich za ta fafata da Real Madrid kan cinikin kyaftin ɗin Chelsea kuma ɗan wasan Ingila Reece James a baɗi. (Fichajes)



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here