BIDIYON | Dake a kafafen sada zumunta wai Aliens sun mamaye jahar Katsina ba gaskiya bane – Yansanda

11
4



An jawo hankalin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo da ke nuna yadda wasu halittu (baki) suka mamaye Katsina.

Rundunar tana son bayyana a fili cewa abubuwan da ke cikin bidiyon gaba daya na bogi ne da kuma kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da mutanen jihar ke samu ta hanyar wata barna.

Don haka, ana kira ga jama’a da kada su firgita su yi watsi da faifan bidiyon na bogi da abubuwan da ke cikin sa.

SP Gambo Isah, ANIPR,
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda,
Domin: Kwamishinan ‘Yan Sanda,
Rundunar Jihar Katsina.

source

11 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here