Babu Yadda Nijeriya Zata Cigaba Bayan Rabin Yan Kasar Na Fama Da Talauci-Peter Obi – Dimokuradiyya

0
3


Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba ba yayin da fiye da rabin al’ummar kasar ke fama da talauci.

Obi wanda ya bayyana hakan a ranar Talata cikin wata sanarwa da ya fitar domin bikin ranar kawar da fatara ta duniya ta bana, ya bayyana yawan talauci a kasar a matsayin barazana ga tsaron kasa.

Peter Obi

A wani bangare na kokarin kawar da talauci, Obi ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su dauki matakan gaggawa da inganci don saka hannun jari a fannin kiwon lafiya da ilimi.

Ya ce yayin da muke bikin ranar kawar da fatara ta duniya a yau, na maido da jajircewata da burina na fitar da miliyoyin ‘yan Najeriya daga kangin talauci a wani bangare na manufata a sabuwar Najeriya.

Karanta nanZamu Farfado Fa Fannin Ilimin Jahar Zamfara Da Ya Dade Da Mutuwa-Dauda Lawan

Kasar mu ƙaunatacciyar Najeriya a yau abin takaici, ana kiranta da ‘babban gidan talauci’ na Duniya.

A bisa ga kididdigar Talauci na Duniya, sama da ‘yan Najeriya miliyan 71 ne ke rayuwa cikin matsanancin talauci a yau kuma jimillar mutane miliyan 133, kashi 63 cikin 100 na al’ummar kasar, suna fama da talauci da yawa a cewar Hukumar Kididdiga ta kasa.

Babu wata kasa da za ta iya ci gaba da fiye da rabin al’ummarta suna fama da talauci inji Obi.

Saka hannun jari a kananun ‘yan kasuwa a duk fadin kasar nan shi ne hanya mafi sauri na fitar da mutane daga kangin talauci, kamar yadda sauran kasashe masu kwatankwacin tattalin arziki kamar Indiya, Bangladesh, China da sauransu suka tabbatar.

A wani labarin kumaKa Kwashe Kayanka-PDP Ta Fadawa Gwamna Sule Na Jahar Nasarawa

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, Indiya ta fitar da kusan mutane miliyan 415 daga kangin talauci tsakanin 2000 zuwa 2021. Sun cimma wannan gagarumin ci gaba ta hanyar rage ma’anar talauci ta duniya.

Cikin girmamawa, ina kira ga gwamnatocinmu, a kowane mataki, da su dauki matakan gaggawa da inganci ta hanyar yin garambawul da saka hannun jari a muhimman bangarorin ci gaba lafiya, ilimi, da fitar da mutane daga kangin talauci.



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here