Yesufu ta ce ba za ta taba goyon bayan Obi ya zama limamin masallaci ba amma ya zama shugaban Najeriya.
Karanta nanA Mulkina Babu Batun Korar Dalibin Jami’a Akan Rashin Biyan Kudin Makaranta-Tinubu
Ta yi nuni da cewa Obi shine dan takarar da zai iya kokawa Najeriya daga masu son ganin an durkusar da kasar.
A wani rubutu da tay a shafinta na X Aisha ta rubut “Naku’ a siyasa ba addini ɗaya ba ne, kabila ko jinsi ɗaya ba. ‘Naku’ shine wanda zai iya ba ku kyakkyawan shugabanci.
Ka ga Mista Peter Obi @PeterObi, ba zan taba goyon bayansa ya zama limamin masallaci ba, amma a matsayinsa na shugaban Tarayyar Najeriya, yana da goyon bayana 100% ko da na kasance mai goyon bayansa daya tilo.
Idan yana son yin takara sau dubu, zan mara masa baya sau dubu. Zan sa a cikin aikin sau dubu da ƙari. Domin a cikinsa ne wanda nake gani yana son sanya aikin da ya dace don kokawa Najeriya daga kuncin wadanda suka rike ta.
A wani labarin kumaBayan Shekaru 7 An Kama Dilan Miyagun Kwayoyi Wanda Ya Tsere Daga Gidan Yari
Maida hankalina shine kokarina. Ba ni da kasuwanci na daina saboda an sace jarin Na mai da hankali kan yadda zan tabbatar da cewa ba a sace nasarar a gaba ba.
Za mu cigaba da gwagwarmayar ganin mun kwato kasar daga halin da ‘yan bani na iya suka sakata a cikin shekaru 8 da suka gabata inji Aisha.