Jagoran adawar Najeriya, ya nemi gaggauta yi wa tsarin mulkin ƙasar gyaran fuska, don hana kotuna abin da ya kira “fakewa a bayan gaza bin ƙa’idojin shigar da ƙara da muhawarorin shari’a masu rikitarwa, suna tabbatar da zaɓen sata da kuma yin zagon ƙasa ga zaɓen al’umma”.
Atiku Abubakar ya ce wajibi ne a mayar da zaɓe da tattara sakamako ta hanyar laturoni, su zama tilas a Najeriya.
Wannan, wani ɓangare ne na taron manema labarai da shugaban adawar, kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya gabatar ranar Litinin a Abuja. Taron na zuwa ne kwana uku, bayan hukuncin kotun ƙoli da ya yi watsi da ƙararsa ta ƙalubalantar nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kotun dai ta yi watsi da ƙararrakin da Atiku Abubakar tare da takwaransa na jam’iyyar LP, Peter Obi suka ɗaukaka, inda ta ce ba su da ƙwararan hujjoji.
Atiku ya ce matsayin Kotun Kolin ko da yake, shi ne ƙarshe, amma dai ya bar baya da ƙura mai yawa.
Ya yi zargin cewa hukunce-hukuncen kotunan zaɓe, sun zaizaye yardar da ‘yan Najeriya ke da ita, ga tsarin zaɓe da kuma dimokraɗiyyar Najeriya.
Ya ce yana mamakin wanda zai shawo kan miliyoyin ‘yan Najeriya, su fita su yi zaɓe nan gaba, bayan sun bi layi sun yi rijista bisa tabbacin da INEC ta ba su, amma sai suka ga an sace ƙuri’unsu, tare da bai wa waɗanda ba su zaɓa ba, nasara.
Dan adawan ya ce idan mutane suka daina yarda, kuma suka dawo daga rakiyar zaɓuka, dimokraɗiyya ta durƙushe ke nan. Kuma ta hanyar tabbatarwa da halasta ci gaba da rashin gaskiya a zaɓuka, kotunan Najeriya, na ƙwace ‘yancin masu zaɓe, na zaɓar wa kansu shugabanni.
Ita dai hukumar zaɓe ta ce ta yi zaɓe cikin gaskiya da adalci, kuma sakamakon hukunce-hukunce da aka yanke a kotuna sun nuna cewa INEC ta taka rawar gani.
Jagoran adawar na Najeriya ya buƙaci ɓullo da tsarin wa’adin mulki ɗaya na tsawon shekara shida kawai ga shugaban ƙasa, wanda ya ce zai riƙa zagayawa tsakanin shiyyoyin Najeriya guda shida.
A cewarsa, hakan zai rage neman mulki ido rufe daga shugabannin da ke kan mulki, da kuma raba musu da hankali.
Sannan matakin a cewar Atiku, zai inganta tsarin raba-daidai da kuma haɗin kan ƙasa.
Haka kuma, in ji jagoran adawan, mulki wa’adi ɗaya zai hana wasu shiyyoyi guda biyu ko fiye, yin babakere, suna raba kujerar shugaban ƙasa a tsakaninsu, da mayar da sauran shiyyoyi saniyar ware.
Atiku ya ce shawarar na cikin muhimman gyaran fuska da aka gabatar wa gwamnatin mulkin soja, wadda ta shirya Babban Taron Tsarin Mulki na Kasa kafin mayar da Najeriya kan tafarkin dimokraɗiyya.
Atiku Abubakar ya kuma bayar shawarar ɗora wa hukumar zaɓe ta Najeriya, alhakin tantance takardun da ‘yan takara da jam’iyyunsu suka gabatar, kuma idan ta gaza yin haka, mai yiwuwa saboda hukumomin da aikin ya rataya a wuyansu ba su yi ba, wajibi ne ta bayyana wa jama’a.
Ya kuma ce ba zai taba ja da baya a kan gwagwarmayar da ya faro ba.
Kuma in ji shi matuƙar yana raye, zai ci gaba da gwagwarmaya tare da ‘yan Najeriya a kan “kyautata dimokraɗiyyarmu da tsarin aiki da doka da kuma sake fasalin siyasa da tattalin arziƙi” da Najeriya ke buƙata don cimma haƙiƙanin bunƙasar arziƙinta.
‘Matasa ne ya kamata su jagoranci gwagwarmaya’
Dan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 da ya wuce, ya ce kamata ya yi matasan Najeriya a yanzu, su jagoranci wannan gwagwarmaya, don kuwa su ne suka fi ruwa da tsaki, a kan masu shekaru irinsa.
Ya ce dole ne dimokraɗiyyar Najeriya ta kasance mai ma’ana, kuma ginshiƙi mai ƙarfi. “Sama da komai, dole ne a aiwatar da ita ta hanyar zaɓuka na gaskiya da adalci, da za su mutunta ƙudurin al’umma.”
Kasashen da ba su kai Najeriya ci gaba ba, in ji Atiku, a wannan ƙarni na 21, suna yin zaɓe da ƙirga ƙuri’unsu ta hanyar laturoni.
Ya ce abu na gaba shi ne dole ne a yi tanadin cewa duk wata shari’ar zaɓe sai an kammala ta, kafin a rantsar da mutumin da ya lashe zaɓen da aka yi.
A cewarsa, irin wannan tsarin Najeriya ta yi amfani da shi a 1979. “Lokacin da ake ɗauka tsakanin zaɓuka da rantsar da waɗanda suka ci zaɓe, ya yi kaɗan a iya kammala shari’o’in zaɓe.”
A cewarsa abin da ake da shi yanzu, daidai yake da cewa ɓarayi su riƙe abin da suka sata, kuma su yi amfani da dukiyar wajen kare kansu a gaban shari’a.
“Kawai yana ƙarfafa gwiwar fashin ƙuri’un mutane ne, maimakon hana yin hakan.”
‘A koma tsarin zaɓe zagaye na biyu’
Jagoran siyasar ya ƙara da cewa don tabbatar da mulkin mafi rinjayen al’umma da wakilci na gaskiya, “dole ne mu koma tsarin da ke neman sai ɗan takarar shugaban ƙasa ya samu aƙalla kashi 51 na ƙuri’un da aka kaɗa” lokacin zaɓe.
Idan kuma ya gaza samun haka, sai dai a tafi zaɓe zagaye na biyu tsakanin ɗan takarar da ya zo na farko, da mai biye masa.
Ya ce akasarin ƙasashen da ke zaɓar shugaban ƙasa, suna amfani da wannan tsari, maimakon irin tsarin Najeriya na zagaye ɗaya.
Kotun, da kuma ɓangaren shari’a, in ji Atiku Abubakar dole ne kuma su kauce wa siyasantar da harkokinsu, kamar yadda al’adar take, ga kusan duk hukumomin gwamnati a Najeriya.
Ya yi iƙirarin cewa batun da Mai shari’a Musa Dattijo Muhammad (wani alƙalin Kotun Koli da ya yi ritaya a kwana-kwanan nan) da kuma tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega suka bijiro da shi, na ƙarin haske ga ‘yan Najeriya a kan dalilan da suka sanya hukumar zaɓe da ɓangaren shari’a suka “kashe kyakkyawan fatan da talaka ke da shi”.
Sai dai, tun bayan zarge-zargen da Mai shari’a Muhammad ya yi, babu martani a hukumance daga ofishin Alƙalin Alƙalan ƙasar. Da kuma hukumomin da ke kula da ɓangaren shari’a a Najeriya.
Atiku dai ya yi zargin cewa ba a naɗa alƙalai bisa cancanta a ƙasar, sai dai bisa muradan siyasa da sanayya.
Ya kuma zargi jam’iyya mai mulki da karkatar da akalar naɗin manyan jami’an hukumar zaɓe, “kamar yadda aka gani a naɗin baya-bayan nan na kwamishinonin zaɓe, inda aka naɗa ‘ya’yan jam’iyya mai mulki da mashawartan ‘yan siyasa na APC a INEC.”
Ya ce idan muhimman hukumomi guda biyu, kamar kotu da hukumar zaɓe suka shiga mugun tarkon harƙallar siyasa, to kusan babu yadda za a yi, a samu bunƙasar dimokradiyya.