Ana Ta Shirin Yanke Hukunci, Kanawa Sun Yiwa Abba Gida-Gida Babbar Tarba a Jihar Kano

0
24


  • Gwamnan jihar Kano ya dawo gida bayan shafe lokaci ba ya cikin jihar da ke Arewa maso Yamma
  • Abba da Gawuna na ci gaba da kai ruwa rana a kotu, an tanadi hukuncin da za a yanke cikin kwanaki masu zuwa
  • Shehi Dahiru Bauchi ya barranta da wata wasikar da ke yawo, inda ake ce ya yi kira ga jojin kasa kan lamarinsu Abba

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al’amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar KanoDubban jama’a ne a ranar Lahadi suka tarbi Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano da ya dawo yankin Arewa maso Yamma, Channels Tv ta ruwaito.

Gwamna Yusuf dai ya yi nesa da jihar ne a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce da kitimurmurar shari’a kan kujerarsa ta gwamna.

Kara karanta wannan

Ba Dani Ba: Sheikh Dahiru ya yi martani kan wasikar da aka ce ya rubuta kan rikicin Abba da Gawuna

Abba ya samu tarbar masoyansa a Kano
Yadda aka tarbi Abba Gida-Gida a Kano | Hoto: @IbrahiemTata
Asali: Twitter

Idan baku manta ba, kotun daukaka kara ta tsige shi sannan ta bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben watan Maris na 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma ya kalubalanci hukuncin kotun tare da garzayawa Kotun Koli, wacce a yanzu haka ta tanadi hukunci kan lamarin.

Abba ya dawo gida Kano

Amma a yau ranar Lahadi 24 ga watan Disamba, jama’a da dama sun kwararo kan titi domin tarbar Gwamna Abba a jiharsa.

Sanye da jajayen hulunan Kwankwasiyya, magoya bayan sun rera wakokin nuna ‘ana-tare’ domin bayyana goyon bayansu ga gwamnan dan jam’iyyar NNPP, rahoton Vanguard.

Wasunsu na dauke da tutoci da fosta da aka rubuta “Abba ne zabin mu” da “Adalci ga Kanawa” a yayin da suka raka ayarin motocin gwamnan zuwa gidan gwamnati.

Hakan dai ya jawo cunkoso saboda yawan jama’ar da ke nuna goyon baya ga gwamnan na Kano da ke fuskantar kalubale mai girma.

Kara karanta wannan

“Kada ka tsoma baki a kitimurmurar da ke tsakanin Abba da Gawuna a Kano”, Dattijan Yarbawa ga Tinubu

Ba dani ba: Shehi ya barranta da wasika kan su Abba da Gawuna

Fitaccen malamin addini a jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman-Bauchi, ya musanta cewa yana da alaka da wata wasika da ke yawo a kafafen sada zumunta mai magana kan batun shari’ar zaben gwamnan Kano.

A cikin wasikar aka ce Shehi ya aika wa babban jojin Najeriya (CJN) Olukayode Ariwoola, malamin ya yi kira ga mai shari’a da ya tabbatar da cewa kotun koli ta yi hukunci a shari’ar da gaskiya, amana da adalci.

A baya an ruwaito yadda hotun koli ta tanadi hukuncin da za ta yanke a karar da aka shigar gabanta na Gwamnan Kano a ranar Alhamis din da ta gabata.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here