Alkalan Alkalai Zai Kafa Kwamitin Alkalan Da Za Su Saurari Karar Atiku, Peter Obi a Kotun Koli

0
2


  • Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour (LP) sun shigar da ƙararraki daban-daban a kotun zaɓe
  • Ƙararrakin sun shigar da su ne domin ƙalubalantar nasarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen 2023
  • Alƙalin alƙalan Najeriya, Kayode Ariwoola, ne zai kafa kwamitin alƙalan kotun koli da zai saurari ƙarar da Atiku da Obi suka shigar a mako mai zuwa

FCT, Abuja – Idan komai ya tafi dai-dai, Alƙalin alƙalan Najeriya (CJN), Olukayode Ariwoola, zai kafa kwamitin alƙalan kotun ƙoli da zai saurari ɗaukaka ƙarar da ta biyo bayan hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban kasa (PEPC).

Idan ba manta ba dai, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Peter Obi da takwaransa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, sun umurci lauyoyinsu da su daukaka ƙara kan hukuncin da PEPC ta yanke a kotun ƙoli.

Kara karanta wannan

Nasarar APC Ta Fara Tangal-Tangal, Kotun Zaɓe Ta Tanadi Hukunci Kan Zaben Gwamnan Arewa

CJN zai kafa kwamiti kan karar Atiku, Obi
CJN zai kafa kwamitin alkalan kotun koli sati mai zuwa
Hoto:.Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

CJN zai kafa kwamitin alƙalan kotun ƙoli

Jaridar Punch ta ce ƴan takarar suna da kwanaki 14 daga ranar da aka yanke hukuncin a kotun don shigar da ƙara a kotun ƙoli. Wa’adin hakan zai ƙare a ranar Laraba, 20 ga watan Satumban 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har yanzu Ariwoola bai kafa kwamitin alƙalan kotun ƙoli da zai saurari kararrakin ba, sai dai jaridar ta ce CJN zai kafa kwamitin a ranar Laraba, lokacin da wa’adin gabatar da kararrakin zai kare.

Ta ambato ɗaya daga cikin majiyoyin kotun yana cewa:

“Ya zuwa yanzu babu wani bayani game da kwamitin ko alƙalan da za su kasance a cikin kwamitin.”

“Abin da muka sani shi ne, za a iya bayyana sunayen mambobin kwamitin a wannan makon, idan an cika ya kai ranar Laraba.”

An Samu Cigaba a Mulkin Obasanjo

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanatan PDP, Ta Yi Fatali Da Karar Yan Takarar APC Da LP

A wani.labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana wa’adin shugaban ƙasan da aƙa fi samun bunƙasar tattalin arziƙi a ƙasar nan.

El-Rufai ya bayana wa’adin mulkin Obasanjo na ɓiyu a matsayin wanda ya fkowane nasara a tarihin ƙasar nan, ta fannin samar da ayyukan yi da rage hauhawar farashin kayayyaki.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here