2027: Ta Yiwu Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Hade da El-Rufai, Hadimin Atiku Ya Magantu

0
12


  • Yayin da ake ta shirin siyasar 2027, an yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi zai hade da Nasir El-Rufai a jam’iyyar SDP
  • Kakakin kamfe na dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar shi ya bayyana haka a yau Juma’a 22 ga watan Maris a shafin X
  • Daniel Bwala ya ce Obi zai bar jam’iyyar LP ne yayin da kungiyr NLC ke kokarin kwace ragamar shugabancin jam’iyyar gaba daya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Daniel Bwala, Kakakin kamfen dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya ce akwai yiwuwar ruguntsumin siyasa a kwanakin nan.

Bwala ya ce dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai su na shirin hadewa saboda zaben 2027.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa El-Rufai ya ziyarci ofishin jam’iyyar SDP, jigon APC ya yi bayani

An yi hasashen dan shugaban kasa zai hade da El-Rufai kan zaben 2027
Bwala ya yi zargin Peter Obi zai hade da El-Rufai kan zaben 2027. Hoto: Peter Obi, Nasir El-Rufai.
Asali: Facebook

Wane hasashe aka yi kan Obi, El-Rufai?

Ya ce Obi zai watsar da jam’iyyar LP zuwa SDP saboda rikicin shugabanci da jam’iyyar tasa ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon kakakin ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya ce El-Rufai ya na shirin barin jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

“Ana zargin Peter Obi zai hade da Nasir El-Rufai a jam’iyyar SDP yayin da kungiyar NLC ta shirya kwace shugabancin jam’iyyar LP.”

“Ruguntsumin siyasa zai faru a wannan kwanakin amma babu abin da zai hana Shugaba Tinubu bacci wanda ya san lungu da sakon siyasa.”

– Daniel Bwala

Jita-jitar ficewar El-Rufai daga APC

Wannan hasashe ya biyo bayan jita-jitar da ake yadawa cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai zai bar jam’iyyar APC.

Hakan ya biyo bayan ziyarar sa tsohon gwamnan ya kai a ofishin jam’iyyar SDP a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Hotunan Ribadu da jiga-jigan APC sun ziyarci El-Rufai yayin da ake jita-jitar zai bar jami’yyar

Jita-jita yayin da Ribadu ya ziyarci El-Rufai

A baya, mun ruwaito muku cewa hadimin Shugaba Tinubu a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu ya ziyarci tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Ribadu ya kai ziyarar ce yayin da ake yada jita-jitar cewa El-Rufai na shirin watsi da jam’iyyar APC yayin da ake tunkarar zaben 2027.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here