2027: Jam’iyyar NNPP Ta Amince da Bukatar Atiku Kan ‘Maja’, Ta Gindaya Sharuda Masu Tsauri

0
3


  • A karshe, jam’iyyar NNPP ta amince da bukatar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar
  • Jam’iyyar ta ce ta gamsu da kiran tsohon shugaban kasar amma ta gindaya sharudan don ganin an samu daidaito a tsakani
  • Wannan na zuwa ne bayan Atiku ya kirayi jam’iyyun adawa da hadin kai don kwace mulki a hannun jami’yyar APC mai mulki

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Jami’yyar NNPP ya amince da tayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na hadaka.

Wannan na zuwa ne bayan Atiku ya nemi ‘yan jam’iyyun adawa da su zo a hada kai don kwato mulki daga APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Shari’ar gwamnan Kano: Yan APC sun fara azumin neman nasara yayin da Abba ya garzaya Kotun Koli

Jam'iyyar NNPP ta amince da hadaka da Atiku ya kira don tumbuke APC
Jam’iyyar NNPP ta amince da bukatar Atiku kan maja. Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi, Kwankwaso R.
Asali: Facebook

Mene bukatar Atiku ga jam’iyyun adawa?

Daga bisani, jami’yyar LP ta yi fatali da bukatar ta Atiku inda ta ce babu wata magana da su ka kulla ta maja, Tribune ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukaddashin shugaban jam’iyyar, Abba Kawu Ali shi ya bayyana haka ga manema labarai a yau Talata 21 ga watan Nuwamba.

Kawu ya ce NNPP ta shirya yin maja da dukkan jam’iyyun adawa amma da sharadin duba bukatun al’umma da dimukradiyya.

Ya ce kiran da Atiku ya yi abun a yaba ne ganin yadda jami’yyar APC ke son mayar da kasar tsarin jam’iyya daya, Vanguard ta tattaro.

Mene martanin NNPP kan bukatar Atiku?

Ya ce:

“Kwanan nan Atiku ya kirayi maja tsakanin jam’iyyun adawa don ruguza tsarin jami’yya daya da APC ke yi a kasar.

“Jam’iyyar NNPP ta karbi wannan kira na Atiku a matsayin kishin kasa kuma abin a yaba.

Kara karanta wannan

Da gaske na hannun daman Atiku ya sauya sheka daga PDP zuwa APC? gaskiya ta bayyana

“Mu na maraba da wannan kira na tsohon shugaban kasa, sai dai dole tsarin ya zamo zai amfani ga bukatun al’umma.”

Atiku ya bukaci yin maja don tunbuke APC

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bukaci hadin kan jam’iyyun adawa don kwace mulki a hannun APC.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya yi nasara a kotun koli kan shari’ar da jam’iyyun adawa su ka shigar.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here