Hukunce-hukuncen Ganin Watan Ramadan

0
9
Hukunce-hukuncen Ganin Watan Ramadan


A’uzu billahi minash shaidanir rajim, bismillahir rahmanir Rahim. Allahumma Salli ala Sayyidina Muhammadin Alfatihi lima uglika wal khatimi lima sabaka nasiril hakki bil hakki, wal hadi ila siradikal mustakim wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim. Wa radiyallahu an as’habi Rasulullahi (SAW), wa la haula wala kuwwata illa billahil aliyyil azim. Ya himmatas Sheikh, ihdirilana bi hazal mahdari wal ta’adifi binazaratin ta’ati lana bizzafari.

Alhamdu lillah. Mun gode Allah da ya nuna mana karatowan wannan sabon wata na Ramadana, wata mai alkhairi, mai albarka, wata mai dukkan wani abu na falala da za a fada, muna fata wurin Allah ya azurta mu da azumtarsa, Allah ya buda wa al’ummar musulmi da abin da za a ci, a sha, Allah ya dauke mana dukkannin musifu albarkacin wannan watan.

Muslim ya fitar da Hadisi daga Abdullahi bin Umar ya ce manzon Allah (SAW) ya yi magana a kan azumi, cewa “Inna ummatan ummiyyatan – mu al’umma ce ba’umma” sai da ya yi ishara da hannunsa, yana nuni da yatsun hannayensa guda goma, ya yi nuni da su sau biyu, na ukun sai ya kulle babban yatsarsa, yana nufin tara (goma sau biyu, sai tara), Annabi (SAW) yana nufin in kuka yi azumi 29 aka ga wata ku sha ruwa, (Sumu li ru’uyatihi, wa afdiru li ru’uyatihi, wa’in gumma alaikum fakdiru salasina – ku yi azumi in an ga wata, ku sha ruwa in an ga wata, idan ba a ga wata a 29 ba, ku kudurce yin Talatin).

Wurin maganar ganin wata, kowacce kasa ana yi mata hukunci ne da Sarkin Musulmi, duk masarautun da ke karkashinsa sai su ba shi rahoton ganin watan, in wancan garin ba su gani ba wani garin za su gani, in Sarki ya yarda, azumi ya zama farilla a kan duk musulmin garin amma in duk garuruwan ba a gani ba sai a shirya cika talatin.

Har ila yau yana daga hukuncin shari’a, ba a fara azumi da kokwanto, misali ka kwanta bacci sai ka kudirce a ranka cewa in an bayyana ganin wata ina bacci, zan tashi da azumi. Mun gode Allah, yanzu sabida na’u’rar zamani da wuri ake sanar da ganin wata.

Lamarin ganin watan Ramadana abu ne mai sauki, sabida galibin Malamai da Shehunnanmu na kasa da waje baki daya suna kan Hadisin Kuraibu da yake cewa “Kowacce kasa da ganin watanta, misalin kasar: Nijer da Ghana, Mali, Togo da dai sauransu duk suna da Sarkin Musulmi kuma shi zai ayyana ganin watan.

Amma kuma, in Nijer suka ga watan Ramadana, Sarkin Musulmin Nijeriya in yaga dama zai iya cewa na ga wata da ganin watan Nijer sabida dare da lokutan kasashen duk iri daya ne. Sai dai ban da kasar da lokutansu ba iri daya ba ne – ra’ayin wasu malamai kenan.

Amma a wannan zamani na kimiyya da fasaha, Allah shi ne zamani. Annabi ya ce ba ma Hisabi, ba ma Rubutu (ba wai ya hana ba ne) Littafinsa ne ma ya yi nuni da a yi Karatu “Ikra’a” Allah kuma ya yabi masu Rubutu “Bi’aidi safarah, kiramin bararah” sabida muhimmancin karatu da rubutu, a ranar yakin Badar, Annabi (SAW) ya yanke wa duk fursunoni fansa amma ya ce duk wadanda suka iya karatu da rubutu su karantar da yaran Madina, wannan shi ne fansarsu.

Allah ya kawo Kimiyya da fasaha da za a iya ganin abin da ido ba zai iya gani ba daga nesa (Telescope) sabida haka duk duniyar Malaman Musulunci suka yi fatawa cewa yanzun in Makkah ta ga watan Ramadana to duk Musulmi su dauki niyyar azumin.

In Sarkin Musulmi ya ga dama ya yi amfani da hadisin kuraibu, tafiyar iyaye da kakanni cewa kowacce kasa da ganin watanta, Sarkin Musulmi ya yi dai-dai, in ya amshi sabuwar fatawa, sabida Hadisin “Sumu li ru’u’yatihi, wa afdiru li ru’u’yatihi – ku yi azumi in kun ga wata sannan ku ajiye in kun ga wata.” Hadisin ya nuna cewa Annabi (SAW) ya hade Jama’arsa duka gaba daya.

In an ce Makkah, kar ka kalli wadanda suke cikin garin, ka yi amfani da garin, shi ne wanda Annabi ya zauna a ciki, tushen Addinin Musulunci.

Dangane da garuruwan da ba su da dare kuwa, kullum rana ce, su kaddara wata, su yi amfani da lokaci, a tsakiyar rana amma lokacin sahur ne ko kuma a tsakiyar rana amma lokacin shan ruwa ne.

In wani musulmi ya ga wata amma Sarkin Musulmi bai amsa maganarshi ba, to shi wanda ya ga watan azumin ya hau kanshi, sai ya azumci azumin a boye sabida girmama hukuma. Addini ya hana Jama’a ta zauna ba shugabanci.

Hadisin kuraibu, tulin Malamai da Shehunnai suna kan wannan Hadisin kuma wayayyu ne sun yarda da zamani.

Hadisin Kuraibu, Muslim ne ya ruwaito shi kuma ingataccen Hadisi ne, Ummul Fadli binti Haris, Matar Abbas dan Abdulmudallib ce ta aiki Kuraibu Sham, wajen Mu’awiya. Kuraibu yake cewa, bayan na isar da sakonta ina Sham, sai azumi ya riske ni ina can, mun ga jinjirin watan Ramadana ranar Alhamis da dare, bayan na dawo Madina, sai Abdullahi dan Abbas ya yi mun zance kan watan, ya tambaye ni yaushe muka ga watan Ramadana a Sham, sai na ce masa ranar Alhamis da dare, sai ya ce min kai ma Allah ya azurtaka da ganin shi? Na ce masa eh, Jama’a da dama sun gan shi, har Khalifa Mu’awiya ma ya yi Azumi, Abdullahi dan Abbas ya ce masa amma mu sai daren Asabar muka ganshi, kuma za mu ci gaba da azumi har sai mun yi 29 ko 30, Kuraibu ya ce masa shin ba za ka wadatu da ganin wata da azumin Khalifa ba, Abdullahi ya ce a’a, ba zan wadatu da ganinsu ba, haka Annabi (SAW) ya umurce mu, kowacce al’umma da ganin watansu.

Wannan Hadisi ingatacce, galibin malamai suna kan shi amma malamai na zamani masu ilimi da fahimta sun tafi cewa tun da Allah ya kawo wadannan ci gaba na kimiyya da fasaha, ba laifi in Sarkin Musulmi ya yarda da ganin watan Makkah ya ce al’ummar Musulmi na duniya su tashi da azumi a rana daya.

An karbo daga Hafsatu Ummul Muminina ta ce Manzon Allah (SAW) ya ce “Duk wanda bai yi niyyar Azumi ba kafin Asubah, bai da azumi”

Ba laifi, mutum zai iya kudurce niyyar yin azumin Ramadana 29 ko 30 a daren azumin farko bayan an sanar da ganin watan ko kuma ya kudurce niyyar azumin ko wacce rana na daga watan ramadana din. Amma ka kwanta bacci da nufin cewa in an ga watan zan ci gaba da azumi in ba a gani ba shikenan, hakan shari’ah ba ta yarda ba.

Allah ya ba mu damar azumtar wannan azumin gabaki daya, Allah ya buda wa ‘yan uwa musulmin duniya da abin da za su ci su sha, Allah ya bai wa kasarmu Nijeriya zaman lafiya. Allah ya saka wa iyayenmu na Zawiyya da alkairi wanda da albarkarsu da karfin Allah muke gudanar da wannan lamarin.



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here