Jagoran NNPP Ya Maida Zazzafan Martani Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara Na Tsige Gwamna Abba

0
4
Jagoran NNPP Ya Maida Zazzafan Martani Kan Hukuncin Kotun Daukaka Kara Na Tsige Gwamna Abba


  • Jagora kuma wanda ya kafa jam’iyyar NNPP ya maida martani kan hukuncin tsige Abba Gida-Gida da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi
  • Dakta Boniface Aniebonam, ya bayyana cewa babu mai hurumin kalubalantar zaman Abba mamban NNPP sai ɗan jam’iyya
  • Ya roƙi ɗaukacin mambobin NNPP musamman mazauna Kano su ƙara hakuri da wannan jarabawar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al’amuran yau da kullum

FCT Abuja – Babban jigon siyasa wanda ya kirkiro New Nigeria Peoples Party (NNPP), Dakta Boniface Aniebonam, ya nuna kaɗuwa bisa hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara na tsige Gwamnan Kano.

Jagoran NNPP, Boniface Aniebonam tare da Abba Kabir Yusuf
Hukuncin Tsige Abba Kabir Yusuf Babban Abun Kaɗuwa Ne, Jigon NNPP
Hoto: Dr Boniface Aniebonam, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ya bayyana hukuncin da Kotun ta yanke ranar Jumu’a 17 ga watan Nuwamba, 2023 a matsayin abin kaɗuwa da takaici, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya maida martani kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a Abuja

Da yake martani kan rushe takarar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kotun ta yi, Aniebonam ya jaddada cewa NNPP ce kaɗai ke da ikon tantance mambobinta ba shari’a ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwan da ya fitar ranar Asabar, babban jigon da ya kafa NNPP, Dakta Aniebonam ya ce:

“Abinda na sani shi ne NNPP da ‘ya’yanta ne kaɗai ke da hurumin tantance su waye mambobinta, na san cewa jam’iyya na iya yiwa mutum alfarma, ta tsaida shi takara a zaɓe.”

“Haka nan kuma na yi imani cewa wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar NNPP ne kaɗai zai iya kalubalantar kasancewar wani mamban jam’iyyar a zabe. Saɓanin haka babu mai hurumi.”

Wanda ya kafa NNPP ya ce jam’iyyar na da ikon daukar nauyin duk wani dan takara ta hanyar yi masa alfarma da ba shi damar tsayawa takara a karkashin inuwarta.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Manyan dalilai biyu da suka sa kotun ɗaukaka ƙara ta tsige Gwamna Yusuf na jihar Kano

Zamu kwato haƙƙin mu a Kotun koli – Aniebonam

Jagoran NNPP ya kuma bayyana kwarin guiwa da fatan cewa gaskiya za ta yi halinta a Kotun ƙolin Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

Ya buƙaci mambobin NNPP da mazauna jihar Kano da su ƙara hakuri da wannan kalubale da ake fuskanta a shari’ar zaɓen gwamna Yusuf.

“Fatan mu na nan yayin da muke tunkarar hukuncin Kotun ƙoli nan ba da jimawa ba,” in ji shi.

Gwamnatin Tinubu ta sanar da kuɗin kujerar Hajjin 2024

A wani rahoton kuma Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa Musulmai za su biya N4.5m a matsayin kuɗin kujerar hajji mai zuwa 2024.

Hukumar kula da jin daɗin maniyyata (NAHCON) ce ta sanar da haka a wata sanarwa, ta kuma sanya wa’adin biyan kuɗin.

Asali: Legit.ng





Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here