Peter Obi ya Magantu kan batun Karatun Shugaba Tinubu

0
4
Peter Obi ya Magantu kan batun Karatun Shugaba Tinubu


Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, Peter Obi ya yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya wanke kansa ta hanyar “gayawa ‘yan Najeriya wanene shi.”

Peter Obi ya ce cece-kucen da Jami’ar Jihar Chicago ta haifar a baya-bayan nan bai dace ba.

Ya ce, “Shugaba Tinubu ne kadai zai iya kawar da cece-kucen da ake ta yi dangane da sunan sa.”

Talla

Tsohon Gwamnan na Anambra ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Laraba a Abuja.

Jami’ar ta saki bayanan karatun Tinubu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar bayan shafe makwanni ana takaddamar shari’a akai .

Gwamnati ta rushe shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Katsina United

A ranar Juma’a ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya shigar da takardun da jami’ar ta bashi a matsayin sabbin shaidunsa ga kotun kolin Nigeria.

Atiku da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, sun shigar da kararraki 86 na daukaka kara a kotun koli don soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ya tabbatar da nasarar Tinubu.

Babu Wani Gari a Borno da ke karkashin Boko Haram – Zulum

Da yake magana a ranar Laraba, Obi ya ce lamarin ya zubar da kimar ‘yan Najeriya a duniya.”

Obi ya ce “‘yan Najeriya sun cancanci sanin ainihin abun da ta shafi shugabansu.”

Ya kara da cewa: “Ya kamata shugaban kasa ya fito fili ya bayyana sunansa, shekarunsa, inda ya yi makaranta da wadanda ya yi makaranta tare da sauran su.

Talla

Cikin girmamawa, ina rokon ka fiti ta yi mana bayani akan wannan batu a yanzu.”



Source link

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here